Kungiyar Hizbullah ta yi wa Isra’ila martani kan kisan Al-Arouri

Hizbullah
Hizbullah

Kungiyar Hizbullah a Lebanon ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa bangaren da cibiyar kula da sararin samaniyar Isra’ila take.

Da safiyar ranar asabar ne Hizbullah ta harba makaman da ta bayyana a matsayin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa mataimakin shugaban kungiyar Hamas a Beirut, Saleh Al-Arouri.

Karanta wannan: ‘Yan sanda sun kama matashin da ake zargi ya yi wa ‘yar uwarsa ciki kuma ta mutu a Kano

Cibiyar Meron wadda ke kan tsaunin Jarmaq da ke arewacin kasar guda ce cikin cibiyoyi biyu da Isra’ila ke amfani da su wajen lura tare da kare sararin samaniyarta.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce cikin wata sanarwa da Hizbulla ta fitar ta ce ”a wani martani na kisan Sheikh Saleh Al-Arouri da wasu ‘yan uwansa a kudancin birnin Beirut, kungiyar ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami a kalla 62 kan cibiyar kula da sararin samaniyar Isra’ila ta Meron.

Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Shugaba Felix Tshisekedi ya sake lashe zaben kasar Congo

Sanarwar ta kara da cewa kungiyar ta samu tabbacin cewa makaman sun shafi cibiyar.

AFP ya ce sojojin Isra’ila sun bayyana kakkabo hare-haren makamai masu linzami kimanin 40 da aka harbo daga kasar Lebanon a safiyar Asabar a bangaren cibiyar Meron.

An yi ta jin karar na’urar ankararwa a biranen da ke arewacin Isra’ila da bangaren Tuddan Gola.

Karanta wannan: Mambobin Hizbullah hudu sun kwanta dama a wani hari ta sama

A ranar Talatar da ta gabata ne wani harin jirgi maras matuki a birnin Beirut ya yi sanadin kisan Saleh Al-Arouri.

Tuni dai hukumomin Lebanon da kungiyar Hamas da Amurka suka zargi Isra’ila da kaiwa harin, to sai dai Isra’ila ba ta dauki alhakin harin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here