Akanta Janar ta Kasa ta ce ba ofishinta ne ke biyan kudin ayyukan da ma’aikatu ke aiwatar ba

Oluwa
Oluwa

Babbar Akanta Janar ta Kasa Dakta Oluwatoyin Madein, ta ce ba ofishinta ne ke biyan kudin ayyuka ko wasu shirye-shirye da ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke aiwatar ba.

Dakta Madien na martani ne kan rahotonnin wasu kafofin yada labarai game da wata bukata daga ma’aikatar jin kai, ta biyan kudin tallafi ga wasu masu karamin karfi a wasu jihohin kasar nan.

Karanta wannan: Gwamna Zulum ya nada sabon Akanta Janar

Ta ce ana ware wa kowace ma’aikata da hukuma kudadenta a asusun ta, kamar yadda yake kunshe cikin kasafin kudin kasa, kuma kowace ma’aikata ita ce ke da alhakin gudanar da ayyukanta da biyan kudin ayyukan da ta aiwatar.

Takarda

 

Cikin wata nasarwa da ofishin babbar akantan ya fitar, ta ce duk da ofishinta ya karbi takardar bukatar biyan kudaden daga ma’aikatar jin kai, amma ofishinta bai biya kudaden ba.

Takarda

Oluwa Shafin X, Akanta, Janar
Dakta Oluwatoyin Madein, ta ce ba ofishinta ne ke biyan kudin ayyukan da ma’aikatu da hukumomi ke aiwatar ba

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 100 kan shirin ciyar da ɗalibai

Ta kara da cewa ofishin nata ya shawarci ma’aikatar kan matakan da za ta bi wajen biyan kudaden kamar yadda dokar biyan kudade ta tanadar.

Babbar Akantar ta kuma ce a irin wanna yanayi, ma’aikatun da abin ya shafa ne ke biyan kudaden zuwa asusun mutanen, ba tura makudan kudade zuwa asusun wani mutum da sunan kudin gudanar ayyuka ba.

Ta kara da cewa a irin wannan biyan kudi ya kamata a tura kudin zuwa asusun mutanen da ake bai wa tallafin.

Sanarwar ta kuma jaddada aniyar Dakta Made na yin aiki bisa doka ba tare da rufa-rufa ba.

Ta kuma shawarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ako da yaushe su tabbatar da suna bin doka da oda wajen gudanar da harkokin kudade.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here