An mayar da Nnamdi Kanu gidan yari a Sokoto – Lauya

nnamdi kanu sad 2

Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya koma gidan gyaran hali na jihar Sokoto daga wajen da ake tsare da shi a hukumar DSS da ke Abuja, kamar yadda tsohon lauyansa kuma mai ba da shawara, Aloy Ejimakor, ya bayyana.

Ejimakor ya ce matakin ya tayar da damuwa saboda ya nisantar da Kanu daga lauyoyinsa, iyalansa da magoya bayansa, yana mai cewa akwai bukatar a sake duba dalilin kai shi wani wuri mai nisa daga cibiyar shari’arsa.

Ya yi nuni da cewa wannan mataki ya sa ake tambaya kan dacewar mayar da Kanu Sokoto, yana mai cewa akwai hanyoyin da gwamnati za ta iya bi don dakatar da abin da ya kira da tabarbarewar yanayin da ake ciki.

Jaridar Punch bai tabbatar da wannan batu ba a daren Juma’ar da aka wallafa labarin.

Kanu ya fara fuskantar tuhuma tun shekarar 2015 kan zargin laifukan cin amanar kasa, ta’addanci da wasu laifuka da suka shafi jagorancinsa a kungiyar IPOB wadda aka ayyana a matsayin haramtacciyar kungiya.

Karanta: Kotu ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai

A ranar Alhamis kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai kan tuhume-tuhume guda bakwai da suka shafi ta’addanci, hukuncin da kungiyar IPOB ta yi watsi da shi tana mai cewa ba ya bisa doka kuma yana da tasirin siyasa.

Alkali James Omotosho ya bayyana cewa saka Kanu a gidan gyaran hali na Kuje ba zai dace ba saboda matsalolin tsaro, wanda hakan ya sa aka nemi wani wuri mafi dacew domin tsare shi.

Lauyan gwamnatin tarayya, Adegboyega Awomolo, wanda ya jagoranci gurfanar da Kanu, ya yaba wa hukuncin, yana mai cewa ya nuna babu wanda ya fi karfin doka a kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here