Da ɗumi-ɗumi: Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnoni shida na APC a Aso Rock

Bola Tinubu Tinubu uk 750x430 (1)

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin ya gudanar da wata ganawar sirri da gwamnoni shida da aka zaɓa a jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sai dai ba a bayyana dalilin taron ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Gwamnoni da suka halarta sun ƙi yin magana da manema labarai bayan fitowarsu daga wurin zaman.

Gwamnonin da suka halarci ganawar sun haɗa da Umar Namadi daga Jigawa, Monday Okpebholo daga Edo, Biodun Oyebanji daga Ekiti, Usman Ododo daga Kogi, Aliyu Sokoto daga Sokoto da kuma Dr Nasir Idris daga Kebbi.

An gudanar da zaman ne a ofishin shugaban kasa, inda taron ya ɗauki tsawon kusan sa’o’i biyu kafin a kammala shi.

Sai dai babu wani jami’in fadar gwamnati da ya bayyana dalilin ganawar, duk da cewa an gudanar da ita ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar karuwar kalubalen tsaro a sassa daban-daban.

Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake gudanar da tuntubar siyasa a faɗin ƙasa da shirye-shiryen jam’iyya da na gwamnati kafin muhimman al’amuran da ake sa ran gudanarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here