Gwamna Bago ya karɓi ɗalibai 100 da aka sace a jihar Niger bayan sakin su

Niger school abduction 1

Gwamnan jihar Niger Umaru Bago ya karbi ɗalibai 100 da aka sace daga makarantar st. Mary’s Catholic da ke Papiri bayan nasarar ceto su da gwamnatin Tarayya ta yi.

Yaran sun isa gidan gwamnatin jihar Niger da misalin ƙarfe 5:20 na yamma a ranar litinin, inda gwamna Umar Bago tare da jami’an gwamnati suka karɓe su.

Motoci daban-daban ne suka kawo yaran zuwa gidan gwamnati, sannan ofishin mai bai wa gwamnati shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya mika su ga gwamnatin jihar, wanda Abdullahi Idi Hong ya wakilce shi.

Jami’an tsaro sun bayyana lokacin mika yaran cewa aiki mai zurfi ya gudana tun bayan sace su domin tabbatar da dawowarsu cikin aminci, tare da nanata kudurin gwamnatin tarayya na kare lafiyar dukkan yara a fadin ƙasa ta hanyar ingantattun matakan tsaro.

Gwamna Bago ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu da Nuhu Ribadu saboda gaggawar da ta taimaka wajen samun sakamakon ceton yaran, inda ya tabbatar wa iyaye da jama’a cewa ƙoƙari na ci gaba don kubutar da sauran ɗaliban da ke hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamnan ya bayyana wannan lokaci a matsayin muhimmin tarihi ga jihar Niger, yana mai bayyana damuwarsa kan ƙarancin shekaru da yawan yaran da suka dawo, sannan ya umarci ma’aikatan lafiya su gudanar da cikakken binciken lafiyar jiki da ta tunani domin tabbatar da jin daɗin yaran.

Gwamnatin jihar Niger tana ci gaba da aiki tare da ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa da UNICEF da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa tsare-tsaren kare yara da tabbatar da dawo da sauran ɗaliban da aka sace cikin aminci, bayan gwamnatin tarayya ta tabbatar da sakin yaran a ranar lahadi.

A farkon ranar litinin, ƙungiyar kiristoci ta ƙasa ta sanar da cewa babu wata sahihiyar bayani da ta karɓa game da sakin yaran kafin daga baya isowarsu gidan gwamnatin jihar Niger ya tabbatar da faruwar lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here