NDA ta gargaɗi jama’a kan takardun shiga har da sojoji na bogi da ke yawo a internet

IMG 20260103 WA0012 768x960 1 750x430

Cibiyar horas da sojoji ta Najeriya (NDA) ta fitar da gargadi game da takardun shiga makarantar na bogi da ke yawo a internet, wadda ke nuna za ta ba da izinin shiga NDA 77 Regular Course (RC).

Jami’in hulda da jama’a na cibiyar Manjo Reuben Kovangiya ya sanar da jama’a a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Kovangiya ya ce, an jawo hankalin NDA ga wasiku na yaudara a halin yanzu suna yaduwa, wanda ake zargin magatakarda na makarantar ya sanya hannu, yana ba da izinin shiga NDA 77 Regular Course (RC).

Koyangiya ya ce an shawarci jama’a da su yi watsi da irin wadannan wasiku ko sakonnin da ke ikirarin ba da izinin shiga NDA.

Ya kara da cewa, yana da kyau a koyaushe a tabbatar da bayanan shiga daga ofishin magatakardar makarantar, ta adreshi academyregistrar@nda.edu.ng.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here