Najeriya ta yi asarar naira tiriliyan 3 sakamakon gobara a shekarar 2021-Minista

4125A066 0AB8 48F6 A3A8 FBACE42D8ED2
4125A066 0AB8 48F6 A3A8 FBACE42D8ED2

Najeriya ta yi asarar Naira Tiriliyan 3 saboda barkewar gobara guda 2,845  a shekarar 2021, in ji Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola.

Aregbesola ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake yiwa sabbin mataimakain Kwanturola-Janar (DCGs) karin girma na hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS) ado.

Ministan ya kuma ce hukumar ta FFS ta ceci kadarorin da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 18.9, da rayuka 587 tare da ceto mutane 260 daga gobarar da ta tashi.

Ya ce, a shekarar 2021, Hukumar kashe gobara ta amsa kiraye-kirayen gaggawa guda 2,845.

“A takaice dai, hannun jarin Hukumar ya karu matuka saboda hukumar ta bayar da gudunmawa sosai ga tsaron kasa wajen kare rayuka da dukiyoyi,” inji shi.

Aregbesola ya ce dalilin da ya sa aka samu irin wannan nasarar shi ne, domin a tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta yi karin kudi gudanar da Hukumar, idan aka kwatanta da tun da aka kafa ta a shekarar 1901.

Ya kuma ce an aike da jami’an kashe gobara 17 zuwa kasar Belarus domin samun kwas din horarwa.

Wadannan jami’an, in ji shi, su ne kwararrun da za su horas da sauran jami’ai kan aikin kashe gobara na zamani, da bala’o’i da kuma kula da gaggawa.”

Aregbesola ya yabawa tsohon shugaban hukumar, Alhaji Liman Ibrahim, bisa hangen nesa da kuma irin gudunmawar da ya bayar ga hidimar, inda ya ce ba zai yi aiki da shi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here