YANZU-YANZU: ‘Yan takara 7 sun yi zanga-zanga, sun bukaci a dakatar da zaben fidda gwani na gwamnan jihar Ekiti

5F3D7626 14DD 4A16 8F73 DC22DC6A7569
5F3D7626 14DD 4A16 8F73 DC22DC6A7569

Bakwai daga cikin 8 da suka tsaya takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a Ekiti, sun yi kira da a dakatar da zaben sa’o’i kadan kafin a fara zaben.

‘Yan takarar guda bakwai tare da magoya bayansu a ranar Alhamis din sun mamaye Sakatariyar jam’iyyar da ke Unguwar Ajilosun a cikin Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekti domin nuna rashin amincewarsu da rashin bin ka’ida.

Sun hada da Sanata Opeyemi Bamidele, Dayo Adeyeye, Femi Bamisile, Bamidele Faparusi, Kayode Ojo, Olusola Afolabi, Demola Popoola da Kayode Ojo.

Sun yi zargin cewa jami’an gwamnatin jihar sun sauka daga tsarin zaben fidda gwani na gwamnoni, inda suka kara da cewa kwamitocin zaben kananan hukumomi jiga-jigan Gwamna Kayode Fayemi ne.

Sun zargi kwamitin zaben fidda gwani na takarar gwamna karkashin jagorancin gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru da yin rashin adalci.

Sun yi zargin cewa an karkatar da tsarin zaben domin dan takarar fa  Gwamna Fayemi ya fi so, Mista Biodun Oyebanji ya samu nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here