Sama da gawawwaki 72 ne aka tsamo bayan gagarumar ambaliyar ruwa.

Ma’aikatan bada agaji a ranar Juma’a sun gano akalla gawarwaki 72 daga wani kauye da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da ambaliyar ruwa ta afkawa.

Gwamnatin lardin a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a lardin Kivu ta Kudu na kasar Kongo ya yi sanadiyyar kawo ambaliya da kogin ya yi sanadin barna da asarar rayuka a kauyukan Bushushu da Nyamukubi.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters a Bushushu ya ce ma’aikatan jin kai da ke tsamo gawarwakin mutane daga baraguzan sun kirga akalla gawarwaki 72, wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara.

A cewar dan jaridar, yanayin ya lafa, inda aka bayyana filayen gidaje da kuma rufin karfen da suka fito daga karkashin laka mai kauri.

Wadanda suka tsira bayan faruwar balahirar sun yi cirko cirko awani bangaren gjnin katako inda ma’aikatan bada agaji na Red Cross sanye da kaya shudi suka tara gawarwaki a saman juna.

Wani jami’in hukumar, Thomas Bakenga ya bayyana cewa akalla mutane 17 ne suka mutu sakamakon ambaliyar kuma mutane kusan 40 sun bata.

Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa ba bakon abu ba ne a lardin Kivu ta Kudu.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, lamarin na karshe na makamancin haka ya faru ne a watan Oktoban 2014, lokacin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje sama da 700 ayayin da sama da mutane 130 ne aka rawaito sun bace a lokacin.

Reuters.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here