Tinubu: Ba na nadama kan cire tallafin mai—Dole ne don gyaran tattalin arziki  

president bola ahmed tinubu 750x430

 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin gwamnatinsa na cire tallafin mai, yana cewa ya zama wajibi don tabbatar da daidaiton tattalin arzikin Najeriya.

A yayin hirar sa da manema labarai a daren Litinin, Tinubu ya ce, “Ba na nadama kan cire tallafin mai. Wannan abu ne da ya zama dole.”

Ya bayyana cewa tsarin tallafin ba zai dore ba, yana mai kwatanta shi da rike makomar kasar don cin moriyar gajeren lokaci.

“Ba mu saka hannun jari, sai dai kawai mun dinga yaudarar kanmu. Wannan gyara ya zama dole. Ba za mu kashe abin da ba mu da kudin shiga don biyansa ba,” in ji Tinubu.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi koyi da tsimin kudi da kyakkyawar kula da tattalin arziki, yana cewa, “Ka yanke tufafi gwargwadon jikin ka.”

Shugaban ya bayyana kalubalen da aka fuskanta daga cire tallafin, ciki har da masu fasakwauri, yana mai jaddada bukatar daukar matakan tsaro da karin gyare-gyare.

Haka kuma, Tinubu ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a turmutsitsin da ya faru a wani taron rabon taimako, yana kira da a kara tsara ire-iren wadannan abubuwan tare da kula da taron jama’a.

“Abin takaici ne a ce mutane ba a girmama su, ko kuma ana zaluntar su a irin wannan yanayin,” in ji shi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here