Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin kawo hargitsi a kasar Nijar

Bola Tinubu new 720x430

 

Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da zargin da gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta yi kan cewa Nijeriyar ta zama wani sansani na musamman domin kawo hargitsi a ƙasar.

zargin da hukumomin Nijar suka yi na cewa dan ta’addar Lakurawa tare da taimakon jami’an tsaron kasashen waje, ciki har da Najeriya ne suka kai harin a Niger-Benin.

Hakazalika gwamnatin Najeriya ta jajantawa gwamnatin Nijar kan mummunan harin da aka kai kan bututun mai.

Kuma ta kara da cewa masu aikata laifin ba su da goyon baya ko taimako daga Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta kuma nuna jajircewa sosai kan lamarin yaki da ta’addanci tana mai cewa ba za ta lamunci ko tallafawa ayyukan irin wadannan kungiyoyi ba.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kuma bayyana damuwa game da aukuwar lamarin.

Hakazalika rahotanni sun bayyana cewa babu sojojin Faransa a yankin arewacin kasar da ke shirin tada zaune tsaye ga gwamnatin Nijar.

Ta kuma kara da cewa yana da mahimmanci a fahimci cewa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa ta kasance ta aminci da kuma girmama juna.

Hakazalika Najeriya za ta ci gaba da binciko duk hanyoyin lumana don kiyaye mutunci da dangantaka da Jamhuriyar Nijar domin amfanin al’umma na kasashen biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here