Ba gudu ba ja da baya game sabuwar dokar haraji – Tinubu

Tinubu, Shugaban, Najeriya, sojoji, kudancin, hukunta, alkawari
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14 ranar 14 ga watan Maris a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren haraji, yana mai jaddada muhimmancinsu ga inganta tattalin arzikin Najeriya.

A lokacin hira ta musamman da ya yi da manema labarai a Lagos, Tinubu ya kare kudirin gyaran harajin da ke kunshe a cikin dokoki da ake tattaunawa a majalisar tarayya, ciki har da dokar haraji ta Najeriya da dokar kafa hukumar haraji.

Ko da yake gyare-gyaren sun fuskanci suka daga wasu shugabannin Arewa, Tinubu ya kare su da cewa suna tallafa wa talakawa tare da kawar da tsoffin tsarin haraji na mulkin mallaka.

Ya ce, “Gyaran haraji ya zama dole, ba za mu ci gaba da dogaro da tsoffin tsare-tsare ba. Talakawa ba za su shiga cikin tsarin haraji ba.”

Dangane da batun raba kudin VAT da ya jawo cece-kuce, Tinubu ya nuna shirinsa na yin tattaunawa amma ya jaddada cewa za a ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren.

Ya ce, “Batun haraji lamari ne na tattaunawa da amincewa har sai an cimma matsaya.”

Shugaban ya kara da cewa kyakkyawan shugabanci yana bukatar yanke shawara mai mahimmanci a lokacin da ya dace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here