Ku bawa matasa takarkaru domin jama’iyyar PDP ta ci zabe – Shekarau

Ibrahim Shekarau 750x430 1

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya kalubalanci jam’iyyar PDP da ta yi amfani da matasan kasar nan wajen lashe mafi yawan kujeru a matakin tarayya da jihohi.

Shekarau ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da kwamitin amintattu na kungiyar shugabannin matasan jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa da na Jiha a Abuja, ranar Litinin.

Ya kuma bukaci matasa da su hada kai da jam’iyyar PDP a matsayin hanyar da ta dace wajen fitar da Najeriya daga dukkan kalubalen da take fuskanta.
Tsohuwar ministar ilimi ta jaddada cewa shekaru 16 da PDP ta yi tana mulki sun fi karfi da inganci ga ‘yan Najeriya

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here