Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta ce ƙudirin da wasu al’ummar mazaɓar sanatan Kogi ta tsakiya suka gabatar mata bai cika ƙa’ida ba.
A makon da ya gabata ne al’ummar mazaɓar suka gabatar da ƙorafinsu zuwa hukumar INEC, inda suka buƙaci yi wa sanatan kogi ta tsakiya Sanata Natasha Akpoti-Uguaghan kiranye daga majalisar dattawan ƙasar.
To sai dai cikin wata sanar da hukumar ta wallafa a shafita na X, ta ce ƙorafin al’ummar mazaɓar bai cika sharadi ba.
Hukumar ta kuma yi alƙawarin bayar da cikakkun bayanai a nan gaba
Labari mai alaƙa: INEC ta sanar da karbar bukatar yiwa Natasha kiranye a majalisar dattawa
A watan da ya gabata ne dai Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da sanata Natasha kan zargin yunƙurin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
A ranar 25 ga watan Maris, INEC ta tabbatar da karbar takardar, tare da buhu shida na takardu da aka ce sa hannun sama da rabin wadanda suka yi rajistar zabe daga mazabar majalisar dattawa 474,554.
Hukumar ta kuma ce ta sanar da Sanatan da aka dakatar game da karbar takardar neman a dawo da ita daga majalisar dokokin kasar. (NAN)













































