Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Abuja a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu, zuwa N’Djamena, Jamhuriyar Chadi, domin halartar bikin rantsar da shugaba Idriss Mahamat Deby Itno.
Bikin rantsar da shi ya biyo bayan ayyana shugaba Deby a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a farkon wannan wata da kotun mulkin kasar Chadi ta tabbatar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce wasu manyan jami’an gwamnati ne suka raka shugaba Tinubu kuma zai dawo bayan kammala bikin.
Karin labari: Yanzu-yanzu: Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudirin komawa tsohuwar wakar kasa
Deby, shugaban mulkin sojan Chadi, ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu, da kashi 61 na kuri’un da aka kada, a cewar sakamakon karshe da aka sanar.
Majalisar tsarin mulkin kasar wadda ta bayyana wanda ya lashe zaben, ta kuma yi watsi da yunkurin da Firaminista Succes Masra ya yi na soke sakamakon.
Masra, wanda ya yi ikirarin samun nasara, ya fada a wani sako da ya aike a kafar sada zumunta cewa bai amince da sakamakon ba amma ya kara da cewa: “Babu wata hujja ta kasa.” Ya yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da zaman lafiya.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin Kano ta amince rushe sabbin Masarautu
Deby ya kira zaben da ya kawo karshen mulkin soji na shekaru uku a wata kasa mai muhimmanci a yakin da ake yi da jihadi a yankin Sahel na Afirka mai fama da rikici.
Deby bai yi wani sharhi kai tsaye ba bayan an ayyana shi ya yi nasara. Amma bayan fitar da sakamakon wucin gadi a ranar 9 ga Mayu, ya ayyana kansa a matsayin zababben shugaban kasar Chadi duka kuma ya yi alkawarin yin kyakkyawan aiki a kan ayyukansa.