Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta amince da wani kudiri na maido da tsohuwar wakar kasa “Nigeria, We Hail Thee.”
Nan da nan aka zartar da kudirin a karatu na daya da na biyu a cikin mintuna.
Muhawarar jagorar maido da tsohuwar waka ta shugaban majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya yi nuni da bukatar ‘yan Najeriya su dauki wakar a matsayin alama ta kasa da kuma alamar iko, wadda ba ta musanta hakikanin gaskiya ba.
Karin labari: Hukumar DSS ta musanta kai hari fadar Sarkin Kano
An maye gurbin tsohuwar waƙar “Nigeria, We Hail Thee” da fiye da ta yanzu da ‘yan ƙasa su ka saba da ita tun a shekarar 1978.
Sai dai shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya nuna adawa da kudirin, yana mai cewa tsohuwar wakar tana da alamar mulkin mallaka wanda shi ne dalilin da ya sa aka kafa sabuwar waka.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin Kano ta amince rushe sabbin Masarautu
Ya yi nuni da cewa ‘yan kasar Britaniya ne suka rubuta tsohuwar wakar, Mista Chinda ya nuna shakku kan muhimmancin sauya wakar a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale mafi muhimmanci a kasar.
Duk da haka, an ba da kudirin doka cikin gaggawa kuma daga baya ‘yan majalisar suka amince da shi.