Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a wani taron maneman labarai da ya yi a fadar gwamnatiN jihar.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin cewa sarakunan da aka sauke su kwashe kayansu daga gidajen sarauta a cikin sa’o’i 48.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin Kano ta amince rushe sabbin Masarautu
Haka kuma duk hakimai da aka daukaka ko aka nada a karkashin dokar da aka soke za su koma kan mukamansu na baya.
Karin labari: Yanzu-yanzu: Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudirin komawa tsohuwar wakar kasa
Gwamnan ya amince da gyara dokar a ranar 14 ga Oktoba, 2020 tare da sanya hannu kan wani gyara a ranar 11 ga Afrilu, 2023.
Sashi na 3 (1) na dokar ya kafa masarautu daban-daban guda biyar da suka hada da Kano, Bichi, Rano, Gaya da Karaye, tare da Karaye suna da ƙananan hukumomi takwas kowacce, yayin da masarautun Bichi da Gaya suke da ƙananan hukumomi 9 kowannensu, Masarautar Rano tana da ikon mallakar fiye da ƙananan hukumomi 10 daga cikin 44 na kananan hukumomi a jihar.
Lokacin da aka tsige Sarki Muhammadu Sanusi, wanda ya jagoranci majalisar a ranar 9 ga Maris, 2020, an yi wa dokar gyaran fuska a karanta: “Akwai shugaban majalisar wanda zai zama sarkin Kano”.
Wani babban jami’in majalisar, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce “babu wani tanadi da zai hana majalisar yin gyara ga doka.”
Zuwa yanzu dai Sarki Muhammadu Sanusi II, shi ne sabon sarkin da aka nada a matsayin dawayya kan karagal mulkin sarautar Kano karo na biyu.