Aliko Dangote na shirin yin ajiye mukaminsa na shugaban kamfaninsa na yin Sikari watau Dangote Sugar Plc, wanda zai kawo karshen shugabancinsa na tsawon shekaru biyu a kamfanin.
Sauka daga mukamin nasa za ta fara aiki ne a ranar 16 ga Yunin bana a cewar wata sanarwa da Sakataren kamfanin Temitope Hassan, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
Dangote ya jagoranci kamfanin tun shekarar 2005, ana kuma yaba wa da sauyawar kamfanin Sikarin na Dangote zuwa jagoran kasuwa a masana’antun sukari a Najeriya.
A lokacin shugabancinsa, ya lura da manyan ayyukan fadadawa da kuma fafutukar inganta ayyukan gudanar da kamfanonin.
“A bisa ka’idojin gudanar da ayyuka nagari na kamfanoni da tsare-tsare na gado, kamfanin Sikarin na Dangote Plc, ya na sanar da mai girma shugaban hukumar Daraktocinmu, Alhaji Aliko Dangote GCON zai ajiye aiki daga ranar 16 ga watan Yuni, 2025,” in ji sanarwar.
Ya kuma kara da cewa, a karkashin jagorancinsa, kamfanin ya samu nasarar aiwatar da wasu muhimman ayyuka na hadin gwiwa a jihohin Adamawa da Taraba da Nasarawa domin bunkasa samar da Sukari a cikin gida da kuma rage dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen waje.
Bayan gudanar da sahihin zabe da mika mulki, hukumar ta nada Arnold Ekpe, tsohon shugaban rukunin bankin Ecobank, a matsayin sabon shugaban kamfanin na Dangote Sugar Plc, daga wannan rana.
Da ta ke maraba da Ekpe kan sabon mukamin nasa, hukumar ta nuna gamsuwa kan yadda zai jagoranci kamfanin zuwa wani sabon zamani, yayin da ta kuma yaba wa Dangote bisa irin jagorancin da yake da shi.













































