Wani Jirgin sama da ke shirin zuwa London ya yi hatsari da dauke da fasinjoji 242

INDIA AVIATION CRASH
This frame grab from a video by @ashlovetea on June 12, 2025 made available on the Eurovision Social Newswire (ESN) platform via AFPTV shows a plume of smoke rising after Air India flight 171 crashed near the airport in Ahmedabad. The London-bound passenger plane crashed on June 12 in India's western city of Ahmedabad with 242 on board, aviation officials said in what the airline called a "tragic accident". (Photo by @ashlovetea / various sources / AFP) / NO USE AFTER JUNE 24, 2025 17:00:00 GMT - -----EDITORS NOTE --- RESTRICTED TO EDITORIAL USE - MANDATORY CREDIT "AFP PHOTO /@ASHLOVETEA/ESN VIA AFPTV " - NO MARKETING - NO ADVERTISING CAMPAIGNS - DISTRIBUTED AS A SERVICE TO CLIENTS - NO ARCHIVES /

Wani jirgin saman fasinja da ke kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya ya yi hatsari yau Alhamis a birnin Ahmedabad da ke yammacin kasar India dauke da mutane 242 a cikinsa, jami’an kula da zirga-zirgar jiragen sama sun ce a wani abin da kamfanin jirgin ya kira “mummunan hatsari”.

Jirgin Air India mai lamba 171, Boeing 787-8 Dreamliner, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa birnin London Gatwick ya yi hatsari jim kadan bayan tashinsa, in ji jami’ai.

Ministan sufurin jiragen sama na Indiya ya ce ya kadu matuka da hatsarin wanda ya afku a Ahmedabad, inda wani dan jaridar AFP ya ga tarin bakin hayaki a filin jirgin.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar India ta ce, mutane 242 a cikin jirgin da yayi hatsari tare da direbobi biyu da ma’aikatan cikin jirgin guda 10.

Jirgin na Kamfanin Air India ya sanar da samun tangarda tare da neman dauki yayin da ya tashi inda kuma nan take ya rikito in ji Babban Daraktan Kula da Sifurin jiragen sama.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman ta ce, jirgin ya fado ne a wajen kewayen filin jirgi na birnin Ahmedabad.

Ahmedabad, babban birnin jihar Gujarat ne a kasar ta India, wanda ya kasance birni mai dauke da mutane miliyan takwas, kuma filin jirgin saman ya na kewaye da wani yanki mai cike da cunkoso.

Ministan sufurin jiragen sama Ram Mohan Naidu Kinjarapu ya ba da umarnin cewa dukkan hukumomin sufurin jiragen sama da na bayar da agajin gaggawa da su dauki matakan da suka dace.

Tuni dai kamfanin sifurin na Air India ya tabbatar da faruwar hatsarin.

“Cikin alhini da bakin ciki muke tabbatar da cewa jirgin Air India mai lamba 171 da ya tashi daga Ahmedabad zuwa London Gatwick ya yi hatsari a yau,” in ji shugaban Air India Natarajan Chandrasekaran.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here