Gobara Ta Lakume Kasuwar Alaba Dake Legas.

Kayayyakin miliyoyin nairori ne dai tuni suka salwanta yayin wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar Alaba.

Daraktar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, Uwargida Margaret Ogunseye ta tabbatar da faruwar gobarar a babbar kasuwar.

Ta ce, duk da haka ma’aikatan kashe gobara, wadanda aka tura domin kashe gobarar an hana su yin hakan.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, yayin da ‘yan kasuwa da wasu suka yi kokarin tunkarar kawo karshen wutar data lashe dukiya mai tarin yawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here