Majalisar Dokokin Jihar Legas Ta Kaddamar Da Dokar Karbar Harajin VAT, Dokar Hana Kiwo A Fili

lagos state house of assembly
lagos state house of assembly

Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da dokar karbar harajin kayayyaki ta VAT hadi da dokar hana kiwo a fili a jihar.

Majalisar ta amince da dokokin guda biyu ne yayinda daukacin yan majalisu guda 40 suka nuna goyon bayan su akan kudurorin a zaman majalisar na ranar Alhamis, yayinda aka yi musu karatu na 3.

An yiwa kudirin dokar taken “Kuduri domin samar da dokar da zata haramta kiwon shanu a fili a jihar Legas da ta ketare iyaka da shanu ba tare da izini ba da sauran makamantan bukatu.”

Karanta Wannan:DSS Na Tuhumar Abokan Huldar Igboho Biyu da Laifukan Ta’addanci

An kuma samar da dokar da zata kakaba tare da karbar harajin kayayyaki ta VAT da wacce zata kula da dokar da kuma sauran batutuwa masu kama da hakan.”

Tun da fari, shugaban majalisar dokokin jihar Mudashiru Obasa ya bukaci magatakardan majalisar, Olalekan Onafeko da ya aike da kwapin dokar zuwa ga gwamna Babajide Sanwo-Olu domin neman sahalewar sa.

“Ina godewa kowannen ku bisa wannan muhimmin tarihi da muka kafa a yau,” inji shugaban majalisar.

Karanta Wannan:HOTUNA: Shugaba Buhari Ya Isa Jihar Imo Domin Ƙaddamar Da Ayyuka

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa an gudanar da tarukan jin ra’ayoyin jama’a akan dokokin guda biyu a ranar Laraba, yayinda masu ruwa da tsaki suka nuna amincewar su da dokar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here