HOTUNA: Shugaba Buhari Ya Isa Jihar Imo Domin Ƙaddamar Da Ayyuka

PMB Owerri
PMB Owerri

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Owerri na jihar Imo, a wata ziyarar aiki ta yini daya, inda zai kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Gwamna Hope Uzodinma na Imo da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu Maso Gabas kuma Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, da dan takarar gwamnan jihar Anambra a Jam’iyyar APC, Andy Uba ne suka tarbi shugaban, a filin jirgin saman kasa da kasa na Sam Mbakwe.

Sauran mutanen dake filin jirgin saman don tarbar shugaban sun hada da wasu ministoci da hadiman shugaban kasa daga yankin Kudu maso Gabas da Babban Sakataren shirin raya aikin gona na NALDA, Mista Paul Ikonne, da sauran jami’an gwamnatin tarayya da na Jiha.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa ana sa ran shugaban, zai kaddamar da kashin farko na hanyar da ta hada Naze zuwa Nekede zuwa Ihiagwa zuwa Obinze da magudanar ruwa ta karkashin kasa da aka yi amfani da fasahar zamani ta Balloon wajen ginata da kuma hanyar kewaye ta Egheada Bypass.

NAN ta kuma ruwaito cewa kafin shugaban ya bar Owerri ya koma Abuja, zai gudanar da tarurruka tare da masu ruwa da tsaki daga shiyyar Kudu maso Gabashin kasar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here