
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shigar da tuhumar ta’addanci har guda biyar a kan wasu mutane biyu da ake tsare da su saboda taimakawa dan awaren yankin yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho.
An shigar da tuhumar ne a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, bayan sama da watanni biyu da jami’an DSS suka kama tare da tsare mutanen biyu.
Wadanda ake tuhuma da laifin mai lamba FHC/ABJ/CR/305/2021 su ne Jamiu Oyetunji da Amudat Babatunde.
Hukumar DSS ta yi zargin cewa wanda ake kara na 1, Oyetunji, yana da bindigogi domin ayyukan da suka shafi ta’addanci, yayin da ake zargin Amudat ta taimaka wajen yayata ayyukan ta’addanci, ta hanyar amfani da shafin ta na Facebook.
Ta bayyana cewa “Oyetunji, Babatunde, tare da wasu, a 1 ga Yuli, kun shirya aiwatar da ayyukan ta’addanci”.
“Oyetunji, Babatunde da sauran wasu da ba su shiga hannu ba, sun aikata laifin a gidan wani Sunday Adeyemo, (aka Sunday Igboho) da ke yankin Soka a Ibadan, jihar Oyo.
“Sun mallaki haramtattun bindigogi wanda ya saba da sashe na 17 na dokar ta’addanci na 2013.
“Sun mallaki bindigogin da aka haramta ba tare da izini ba, na AK 47 guda biyar, biyu masu lamba 04956, 213740, da wasu guda biyu waɗanda ba a iya tantance lambobinsu ba, sai wasu bindigogin na daban masu lamba 8836 da 9398, da sauran wasu nau’in bindigogi na daban.
A cewarta “Wannan ya sabawa Sashe na 1 (3) (c) (v) na Dokar Ta’addanci (CAP 10, 2011) kuma akwai hukunci ƙarƙashin sashi na 1 (2) na Dokar da aka yiwa gyaran fuska ta 2013.”
Sai dai, ba a sanya ranar da za a saurari karar ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa kotun ta bayar da belin dukkan abokan huldar Igboho su 12 kuma DSS ta saki 10 daga cikin su.
(NAN)












































