Ana harbe mutum guda a kowacce awa daya a Afirka ta Kudu

dafa84e0 0d96 11ed 93ba 314ede9cd985.jpg
dafa84e0 0d96 11ed 93ba 314ede9cd985.jpg

Kwararru a Afirka ta Kudu sun ce ana harbe mutum guda cikin kowacce awa a kasar.

Hakan ya sa mutane suke fama da tashin hankalin da ke biyo bayan harbe-harben bindigar.

“Kwana ake ana jin harbin bindiga. Harbe-harbe a kowanne dare,” in ji wani mazaunin Soweto da bai son a ambaci sunansa.

BBC ta rawitu cewa a wannan garin da ke wajen birnin Johannesburg, aka harbe mutane 15 a wata mashaya a farkon watan nan inda suka mutu nan take. Kwanaki kadan karin wasu suka mutu a gadon asibiti.

Rahotanni sun ce gungun mahara dauke da bingigogi ne suka afka wa mashayar da daddare tare da bude wa mashaya wuta sannan suka tsere.

Wannan harin da wadanda aka ci gaba da kai wa mashaya daban-daban, sun kara fitowa da hadarin da ake ciki a kasar Afirka ta Kudu.

Na kai ziyara yankin Soweto, bayan kashe-kashen, inda na fahimci cewa har yanzu mutane na cikin firgici.

Sai dai suna da kyakkyawan fatan hukumomi za su dauki matakin da ya dace.

 “Tun da na fara zama a wannan yankin shekara da shekaru, ‘yan sanda ba sa zuwa ko da mun kai rahoton bukatar haka. Abin da suke fada mana shi ne, yankin ya fi karfinsu, yana cike da hatsari.

“Ban san dalilin da ya sa suke fadar haka ba, alhalin akwai mutanen da ke zaune a nan,” in ji mutumin.

An dauki makwanni da kai harin, amma har yanzu ba a kama ko da mutum guda ba.

 Sai dai laifukan harbin bindiga ba sabon abu ba ne a Afirka ta Kudu, ko a yankin Soweto.

A nan na hadu da wata uwa a Cape Town, mai suna Lesley Wyngaard, da ke cikin alhini, a yankin da ‘yan bindiga da tashin hankali suka yi wa jama’a kawanya.

“Sun dauke min sanyin idanuna, ba zan sake farin ciki ba har abada,” in ji ta lokacin da ta fashe da kuka, tana yi min bayani kan halin da ta samu kanta a ciki tun bayan mutuwar danta shekaru bakwai da suka gabata.

‘Yan bindiga ne suka kashe Rory, mai shekara 25, ta hanyar harbinsa da bindiga a kai, a wani dare da ya ke hira da abokanshi a Mitchells Plain, a wani lamari na tsautsayi a lokacin da bai dace ba.

Ana yi wa yankin Mitchells Plain kallon unguwar bata-gari, yankin da gungun masu aikata muggan laifuka – kama daga safarar kwaya da sayar da ta, zuwa matattarar ‘yan daba – suke yawan samun hatsaniya, da ke rutsawa da wadanda ba su san hawa, ko sauka ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here