Saudiyya ta yi nasarar cafke ‘Yar kasar Masar mai amfani da shafin TikTok tana yada bidiyon batsa

download 1
download 1

An cafke fitacciyar ‘yar kasar Masar din nan mai amfani da shafin TikTok a kasar Saudiyya kan zargin wallafa abubuwan batsa.

Al Jazeera ta rawaitu cewa Tala Safwan na da mabiya miliyan biyar a shafin TikTok, da wasu 800,000 a shafin Youtube, kuma ta ja hankali ne bayan wallafa wani bidiyo da aka yi amfani da kalaman ‘yan madigo a ciki.

Sai dai Ms Safwan ta ce ba ta yi hakan da wata mummunar manufa ba. ‘Yan sanda a Saudiyya sun ce bidiyon ka iya cutar da wasu, da yada rashin tarbiyya.

Tala na jan hankalin matasa ma’abota shafukan sada zumunta da gajeren nannadadden bakin gashinta.

Bidiyon da take wallafawa na yawan tayar da kura a shafukan intanet, inda takan yi wa mabiyanta jawabi kan batutuwan da suka shafi soyayya da abubuwan da ba su dace ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here