Kano: Uwa Ta Mika Danta Ga ‘Yan Sanda Bisa Neman Sa Da Suke Ruwa A Jallo 

Police badge
Police badge

Wata Mahaifiya a jihar Kano ta mika danta ga rundunar yan sandan jihar Kano bisa neman sa da suke ruwa a jallo.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a jihar.

A cewarsa, Hantar Daba, wanda hukumar ‘yan sandan Kano ta bayar da tukuicin naira 500,000 ga duk wanda ya same shi, ya mika kansa ga hukumar ‘yan sanda.

“Hantar Daba ya mika kansa ne tare da mahaifiyarsa kuma babban abokin hamayyarsa a yanzu, Abba Burakita na Dorayi, shima ya kai kan sa ofishin ‘yan sanda.

“Labari mai dadi shine, mutum na karshe; Hantar Daba, wanda aka yi ta nemansa da aikata laifuka a karshe ya mika kansa ga ‘yan sanda,” in ji Kiyawa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce duk wani mutum ko  wasu mutanen da ke da wani korafi a kan Daba to so zu gaban ‘yan sanda.

Ya ce, duk da haka, Dana ya bukaci ya kasance cikin shirin wadanda gwamnatin kano zata yiwa afuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here