Hukumar kula da Alhazai ta kasa NAHCON ta bude aikace-aikacen hukumomin tafiye-tafiye da ke neman lasisin shiga aikin Hajjin 2026, inda ta yi kira ga masu sha’awar shiga aikin Hajji da su fara rajista kafin ranar 15 ga Satumba, 2025.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun hukumar a ranar Laraba.
Idan dai za a iya tunawa a baya Hukumar Alhazai ta bayyana ranakun da za a gudanar da aikin Hajji, inda ta bayyana cewa mahukuntan Saudiyya sun dage kan cewa ba za a kara wa’adin ba kan ko wanne mataki.
Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ta kuma sanar da hukumar sakamakon keta haddin bizar da ta yi, inda ta kara da cewa maniyyatan da aka samu suna gudanar da aikin ba tare da takardar izinin Hajji ba, za su fuskanci hukunci na Riyal 20,000 (N8.15m) da kuma dauri.
A cewar sanarwar, Hukumar ta jaddada cewa kamfanonin da suka cika ka’idojin hada-hadar su ne kawai za a yi la’akari da su.
NAHCON ta bayyana cewa, dole ne masu neman aikin su kasance masu rijista da Hukumar Kula da Kamfanoni, sannan su mallaki sahihiyar amincewar kungiyar sufurin jiragen sama ta kasa da kasa, tare da kula da kwararrun ma’aikata, baya ga samun ingantaccen shaidar aikin Umrah ko aikin Hajji.
Sannan kuma sun bayyana cewa, masu bukatar sai sun kasance ba su da wani tarihin wani hukumci da wata kotun shari’a a Najeriya ko Saudiyya ta yanke musu, ko kuma wata hukumar alhazai ta Najeriya ko Saudiyya, da hukumomin jiragen sama ko kuma wata hukumar da ke kula da harkokin gwamnati.
Ana kuma sa ran masu neman za su sabunta bayanan kamfanoninsu da hukumar da suka hada da biyan haraji, asusun tantancewa, da cikakkun bayanai na daraktoci da ma’aikatan da ke da alhakin al’amuran Hajji.
Hukumar ta kuma tunatar da masu ruwa da tsaki cewa wa’adin tabbatar da yin rajistar sansanin Masha’ir a Saudiyya shine ranar 4 ga Janairu, 2026













































