Hajiya Rabi Idris da ake kira da Hajiya Umma, mahaifiyar Babban Editan Daily Trust Malam Hamza Idris, ta rasu.
A cewar daya daga cikin ‘ya’yanta, Aminu Idris, ta rasu ne da safiyar yau Litinin, 23 ga watan Yuni, a gidanta da ke Kano sakamakon gajeriyar rashin lafiya.
Ya kara da cewa, za a yi jana’izar ta ne a makabartar Wali Maigeza wadda aka fi sani da Makabartar Kofar Mazugar a cikin birnin Kano.













































