Kotun Daukaka Kara Ta Kori Kakakin Majalisar Nasarawa

Nasarawa speaker
Nasarawa speaker

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi, dan jam’iyyar APC a jihar.

Kotun ta kori kakakin ne a ranar Talatar, inda kotun ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP Sa’ad Abdullahi Ibrahim a matsayin wanda ya cancanta kuma ya lashe zaben yakin Umaisha/Ugya da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Idan dai za a iya tunawa, an yi takun-saka tsakanin kakakin majalisar dokokin jihar, Mista Ibrahim Balarabe-Abdullahi mai wakiltar yakin Umaisha Ugya a majalisar dokokin jihar da kuma Mista Daniel Ogah Ogazi mai wakiltar yakin Kokona ta Gabas sun sami rashin jituwa.

Rikicin da ya barke a majalisar dokokin jihar Nasarawa ya kai ga samun shugabannin majalisar guda biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here