Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice Parradang

Parradang 750x430

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja.

A cewar wata majiyar tsaro ta mai bincike kan al’amuran tsaro Zagazola Makama, an sace Parradang ne a yankin Area 1 da ke Abuja da sanyin safiyar Talata.

Makama ya ce bayan an bi sawun sa daga bankin da ya ciro kudi, maharan sun karbe masa kudin kafin daga bisani su kashe shi.

Parradang, wanda ya yi aiki a hukumar ta NIS sama da shekaru 30, ya rike mukamai daban-daban a fadin kasar nan kuma daga karshe ya zama Kwanturola Janar na Hukumar.

Karanta: Yan bindiga sun sace tsohon shugaban NYSC da wasu mutane a Katsina

Ya yi aiki a Jihohi kamar Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Babban Birnin Tarayya (FCT). Ya kuma halarci kwasa-kwasan kwararru da dama a cikin Najeriya da wajen kasar nan.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, bai yi karin bayani ba game da lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here