Kalubalen Tsaro yasa an sauya matsugunnin Sansanin masu hidimar Kasa a Jihar Zamfara

images 2
images 2

Gwamnatin jihar Zamfara ta mayar da sansanin masu yi wa kasa hidima NYSC daga karamar hukumar Tsafe zuwa Gusau, na wucin gadi sakamakon tabarbarewar tsaro.

Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Muhammad Gusau ne ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin babban daraktan hukumar ta NYSC Birgediya Janar M K Fadah.

Sanata Hassan Gusau ya yi takaitaccen bayani kan yanayin tsaro a jihar, inda ya shaida wa Darakta Janar din cewa, sannu a hankali an fara samun saukin lamarin, yayin da mutane ke ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.

Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi magana da hukumar NYSC kan dakatar da ayyukan sansanoni a jihar sakamakon kalubalen tsaro da ya ta’azzara.

Ya kuma bayyana koma bayan da aka samu a matsayin rashin ci gaba, kuma Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya bayar da umarnin a baiwa hukumar NYSC wajen da take bukata a babban birnin jihar domin a mayar da masu yi wa kasa hidimar can na wucin gadi domin a samu saukin gudanar da ayyukan.

Mataimakin Gwamnan, yayin da yake taya Darakta Janar din murnar nada shi, ya kuma tabbatar masa da kudirin gwamnatin jihar na samar da duk abin da ake bukata domin tabbatar da tsaro a sansanin na wucin gadi.

Da yake jawabi tun da farko, Darakta Janar na hukumar ta NYSC Birgediya Janar M K Fadah, ya ce sun je jihar ne domin duba wurin da aka bawa hukumar na wucin gadi da kuma zabar wuri mafi kyau kamar yadda gwamnatin jihar Zamfara ta amince.

M K Fadah, ya ce da wannan ziyara da kuma tabbacin gwamnatin jihar na ci gaba da tallafawa ayyukan hukumar na yau da kullun za su ci gaba da aiki a jihar nan take.

A cewar Darakta Janar din, kalubalen tsaro a yanzu ya zama ruwan dare gama duniya wanda ya shafi kusan kowace kasa, kuma Najeriya ba ta bar baya da kura ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here