Atiku ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Yan takarar Shugabancin Kasa a PDP

IMG 20220529 WA0002
IMG 20220529 WA0002

Tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe zaben Fidda Gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Jiya Asabar.

Atiku Abubakar ya samu kuri’u 371 inda ya kayar da abokin karawarsa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, wanda ya samu kuri’u 237.

Dayake sanar da sakamakon zaben Sanata David Mark, ya ce jimillar wakilan da aka amince da su sun kai 767, adadin kuri’un da aka kada ya kai 763, yayin da kuri’u 13 kuma suka lalace.

David Mark ya ce “Abubakar ya samu mafi yawan kuri’u a zaben da aka bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara”.

Ya kuma bayyana Gwamna Udom Emmanuel, na jihar Akwa-Ibom a matsayin wanda ya samu kuri’u 38, sai Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da ya samu kuri’u 20.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya samu kuri’u 70 yayin da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim ya samu kuri’u 14.

‘Yar takara mace guda tilo, Uwargida Tari Oliver, da tsohon shugaban kungiyar masu hada magunguna ta Kasa, Mazi Samuel Ohuabunwa, sun samu kuri’a guda-guda.

Sauran ‘yan takarar da ba su yi zabe ba sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da Mawallafin Mujallar Ovation, Dele Momodu, sai tsohon shugaban majalisar jihar Abia, Chikwendu Kalu da kuma tsohon mataimakin kakakin jihar Abia, Cosmos Nekwe.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya janye daga takarar kuma ya fice daga jam’iyyar.

Sauran wadanda suka janye daga takarar sun hada da kwararre kan harkokin kudi, Mohammed Hayatudeen da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da kuma Dakta Nwachukwu Anakwenze.

An haifi Atiku Abubakar a ranar 25 ga watan Nuwambar 1946 a Jada ta jihar Adamawa, ya tsaya takarar gwamnan jihar sau uku a 1990 da 1997 da kuma 1998, lokacin da aka zabe shi kafin ya zama abokin takarar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a 1999, wanda ya ci gaba da zama a matsayin mataimakin shugaban kasa har shekarar 2003.

Abubakar ya yi takarar kujerar shugaban kasa sau da dama, ciki har da 2014, lokacin da ya tsaya takara a jam’iyyar APC kuma ya sha kaye a zaben fidda gwani a hannun shugaba mai ci a yanzu Muhammadu Buhari.

Ya kuma tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a shekarar 2019, amma ya sha kaye a hannun shugaba Buhari na APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here