Hukumar kula da Alhazai ta kasa NAHCON ta bukaci maniyyatan Najeriya da su guji daukar kudaden da suka haura Riyal 60,000 na Saudiyya ko makamancin su domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
NAHCON ta ba da wannan shawarar ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labaranta, Malam Shafil Mohammed, ya fitar a Abuja ranar Laraba.
Mohammed ya gargadi Maniyyatan da su guji daukar makudan kudade.
“Duk wani adadin da ya zarce Riyal 60,000 na Saudiyya ko makamancinsa na karafa masu daraja, duwatsu, ko m zinare, dole ne a bayyana shi a hukumar kwastam bayan isowa da tashi, a sanar da ku, ku zauna lafiya,” in ji shi. (NAN)













































