Najeriya da Saudi Arabiya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna don karfafa hadin gwiwar aiki wajen dakile safarar miyagun kwayoyi.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da kuma babban daraktan hana da sha da fataucin miyagun kwayoyi (GDNC) na masarautar Saudiyya ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Litinin a birnin Riyadh.
Sanarwar da Femi Babafemi, Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA ya fitar, ya ce kasashen biyu sun kuma amince da tsaurara matakan safarar miyagun kwayoyi a yankunansu.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ya ce kasashen biyu sun dade suna kawance a bangarori daban-daban.
Marwa, wanda ya samu rakiyar daraktan ayyuka da bincike na hukumar (DOGI) Ahmed Ningi, ya ce kasashen biyu na da tarihin dangantaka a tsakaninsu.
Ya ce kawancen ba wai batun kulla alaka ne kawai ba, har ma ya kai ga zurfafa dangantaka, kamar yadda aka rattaba hannu a kan yarjejen
Marwa ya yabawa mahukuntan Saudiyya kan tallafin da suka bai wa NDLEA a baya, yayin da ya kuma bayyana wasu fannonin da hukumar za ta bukaci taimakon gwamnatin Saudiyya.
A nasa jawabin, Darakta Janar na Hukumar GDNC ta Saudiyya, Manjo Janar Mohammed bin Saeed Al-Qarni, ya bayyana jin dadinsa da sanya hannu kan yarjejeniyar bayan shafe shekaru uku ana tattaunawa da shirye-shirye.
Sai dai ya yabawa Marwa da tawagarsa bisa jajircewa da gaskiya da suke yi na kokarin shawo kan matsalar safarar miyagun kwayoyi a duniya.
Ya ba da tabbacin jajircewar mahukuntan Saudiyya kan yarjejeniyar, tare da yin alkawarin karin tallafi ga NDLEA a watanni masu zuwa.
Muhimman abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa ta hada da: musayar bayanan sirri tsakanin Najeriya da Saudiyya, Saudiyya za ta baiwa hukumar NDLEA horo na hadin gwiwa, samar da kayan aiki ga NDLEA, gudanar da binciken hadin gwiwa da musayar bayanai kan wadanda aka kama.(NAN)