Gwamnatin tarayya ta bayyana goyon bayanta ga ‘yancin ‘yan kasa musamman matasa na yin zanga-zanga, tare da amincewa da koke-kokensu da kuma muhimmancin fadin albarkacin bakinsu.
Sai dai gwamnatin ta yi gargadi kan duk wani nau’i na lalata ababen more rayuwa yayin zanga-zangar, tare da jaddada bukatar gudanar da zanga-zangar lumana.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Ministan Cigaban Matasa, Kwamared Ayodele Olawande, a Abuja ranar Litinin, yayin da yake amsa tambayoyi daga jaridar Vanguard.
Olawande ya bayyana cewa, yayin da gwamnati ta amince da sahihancin batutuwan da masu zanga-zangar suka gabatar, yana da matukar muhimmanci a ci gaba da gudanar da zanga-zangar cikin lumana ba wai ta rikide zuwa tashin hankali ko lalata dukiyoyin jama’a ba.
Karanta: Yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a Abuja
Da yake bayyana goyon bayansa ga ‘yancin gudanar da zanga-zangar, Olawande ma ya bayyana cewa, da ya samu lokaci, da da kansa zai shiga zanga-zangar.
Ya ce, “Kowa na da ‘yancin yin zanga-zanga, a gaskiya idan na samu lokaci, zan shiga zanga-zangar da kaina, akwai ‘yancin fadin albarkacin baki ga kowa.
Matasan da ke zanga-zangar suna da kwararan dalilai sun ga wasu batutuwa kuma suna jin cewa akwai bukatar su yi magana, shi ya sa suke fitowa kan tituna.