Babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Usman Baba ya bayar da umarnin kulle dukkanin sakatariyar ƙananan hukumomi 17 na jihar Plateau.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Plateau, Bartholomew Onyeka, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Alabo Alfred ya rattaɓawa hannu.
Sanarwar ta yi nuni da cewa an ɗauki wannan matakin ne domin guje wa yi wa doka karan tsaye biyo bayan hargitsin da ya tashi kan naɗin sabbin shugabanni a ƙananan hukumomin da gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ya yi.
“Hakan ya zama wajibi ne saboda hargitsin da ya tashi kan shugabancin ƙananan hukumomin da barazanar da magoya baya da shugabannin ƙananan hukumomin su ke yi kan kayan gwamnati da rayuwa da dukiyoyin al’ummar jihar.”
“A dalilin hakan rundunar ƴan sandan jihar Plateau ba za ta zuba ido ta bari abubuwa su taɓarɓare ba, hakan ya sanya mu ka ɗauki wannan ƙwaƙƙwaran matakin na rufe sakatariyoyin ƙananan hukumomin.”
Rundunar ƴan sandan ta kuma yi gargaɗin cewa ba za ta sassautawa duk wanda ya yi ƙoƙarin hana cika wannan umarnin ko kawo ruɗani a sakatariyoyin ƙananan hukumomin.
A satin da ya gabata ne gwamnan jihar Caleb Mutfwang, ya dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin tare da kansilolinsu domin bayar da dama a gudanar da bincike kan zarge-zargen baɗaƙalar kuɗi da majalisar dokokin jihar take yi musu.
Daga baya gwamnan ya maye gurbinsu da shugabannin kwamitin riƙon ƙwarya amma tsaffin shugabannin waɗanda ƴan jam’iyyar APC, sun yi fatali da dakatarwar da aka yi musu inda suka sha alwashin ci gaba da zama a ofisoshinsu.













































