Kotun koli ta tsaida ranar laraba amatsayin ranar yanke hukunci kan wanene halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Ebonyi a zaben 2023.
Kwamitin shariar me mutum biyar karkashin jagorancin mai shari’a Amina Augie ta ce ana saran zartas da yanke hukuncin ayau da karfe 3 na yamma bayan gabatar da karar da lauyoyi suka gabatar wanda Ifeanyi Chukwuma Odii ya shigar.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa Mista Odii da Sanata Joseph Obinna Ogba sun yi tsayiwar-gwamin-jaki kan kujerar dasuke takaddamar wanda aka zaba a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben shekara mai zuwa a zaben fidda gwani na jam’iyyar da ya gudana a lokuta daban-daban.
A baya-bayan nan ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta bayyana Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya, Ogba a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.
Amma Mista Odii, sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin kotun, ya garzaya tareda shigar da kara a kotun koli.
Kwamitin shariar mai wakilai biyar ya tsaya tsayin daka domin yanke hukunci bayan lauyoyin bangarorin sun amince da tsarinsu tare da gabatar da hujjojinsu.













































