Ƙungiyoyin kishin al’umma sun buƙaci shugaba Buhari ya janye yafe wa mutanen da aka samu da laifin rashawa

R L Joshua Dariye and Jolly Nyame
R L Joshua Dariye and Jolly Nyame

Wasu gamayyar ƙungiyoyin fararen hula na jihohin Arewacin Najeriya, sun yi barazanar ƙada ƙur’un ƙin amincewa da gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, matuƙar ta ƙi janye afuwar da aka yi wa wasu da aka samu da laifin cin hanci da rashawa da suka haɗa da tsoffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba.

Jaridar Solacebase ta ruwaito yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bisa shawarar majalisar dokokin ya yafe wa masu laifi 159 da suka haɗa da tsohon gwamna Joshua Dariye na Filato da kuma tsohon gwamna Jolly Nyame na Taraba.

An ɗaure tsofaffin gwamnonin biyu ne bisa laifin satar biliyoyin naira na kudaden jama’a da kuma hukuncin da kotun ƙoli ta yanke musu.

Wata sanarwa da kungiyoyin fararen hular 19 suka amince da shi tare da hadin gwiwar Ambasada Ibrahim Waiya da Ibrahim Yusuf, Shugaba a ranar Alhamis kuma aka aike wa Solacebase, sanarwar ta yi Allah-wadai da afuwar da aka yi wa mutanen biyu.

Sanarwar ta kuma ce, matakin na da illa ga yaƙi da cin hanci da rashawa kuma zai kashe ƙwarin gwiwar ma’aikatan da ke yaƙi da cin hanci da rashawa.

“Mu mahalarta wannan babban taro, a matsayinmu na jakadun yaƙi da cin hanci da rashawa, muna Allah wadai da wannan mataki gaba ɗaya, muna kuma roƙon mai girma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari GCFR, da ya gaggauta janye matakin da ya ɗauka na yafe wa waɗanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa domin amfanin ƴan Najeriya,” in ji sanarwar.

‘’Idan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kasa janye matakin da ya ɗauka, to zai kasance babu wani zaɓi illa neman goyon bayan sauran ƙungiyoyin farar hula a fadin Najeriya da ma sauran ƙasashen duniya wajen kaɗa kuri’ar kin amincewa da gwamnatin tarayya.

‘’Muna so mu tunatar da mai girma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari cewa yaƙi da cin hanci da rashawa shi ne babban ginshikin alkawurran da ya ɗauka a yaƙin neman zaɓensa da ajandar gudanar da mulki wanda ƴan Najeriya da dama suka yi imani da goyon bayan takararsa ta shugaban kasa.

Sai dai kuma abin takaici shi ne, tun da aka kafa wannan gwamnati a shekarar 2015 ayyuka da manufofin gwamnati a kodayaushe sun saɓa wa ƙoƙarin tallafa wa da ƙarfafa cibiyoyin yaƙi da satar dukiyar al’umma a Nijeriya irin su EFCC fannin shari’a da sauran su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here