Ƙasurgumin ɗan bindigar nan Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su, ya kuma amince ya daina kai farmaki ga manoma bayan ya gudanar da taron zaman lafiya da dama da malaman addinin Musulunci a sansaninsa.
Shahararren malamin addinin Musulunci Malam Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, ne ya bayyana hakan yayin wani taron addini a ranar Litinin a Kaduna.
A cewar Malam Yusuf, Turji ya miƙa wasu makaman sa ne bayan kammala zaman sulhun da aka gudanar a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Ya bayyana cewa mazauna garin Shinkafi sun tuntubi tawagar malaman sa, inda ya bukaci su tattauna da Turji domin su koma gonakinsu da ke cikin dazuzzuka.
Ya ce, an gudanar da tarukan sau uku a watan Yuli a cikin dajin Fakai.
“Mun hadu da Turji da Dan Bakkolo da Bakar fata da Kanawa da Malam Ila, ba gaskiya ba ne rade-radin da ake cewa an kashe Dan Bakkolo, waɗannan mutane ne suke ta’addancin akidar, kuma duk sun amince da shawarwarin zaman lafiya, ɗaya daga yarjejeniyar shi ne su miƙa wasu cikin makamansu domin nuna amincewa da shirin zaman lafiya.
“Sun miƙa makaman ne a matakai uku a lokuta daban-daban, kuma sun bai wa mazauna garin Shinkafi damar shiga gonakinsu a dajin da ke rafin da ke kan hanyar sansanin Turji.
“Ya kuma saki mutane 32 da suka yi garkuwa da su a wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya,” in ji Malam Yusuf.
Ya ce waɗanda aka yi garkuwa da su da suka hada da mata da kananan yara, sun shafe kusan watanni hudu a hannun ƴan bindigar.













































