Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen za a yi tsawa da ruwan sama a fadin kasar daga ranar Litinin zuwa Laraba, inda ta yi gargadin yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a wasu yankunan.
NiMet ta yi hasashen zazzafar tsawa a ranar Litinin, inda ake sa ran za a yi ruwan sama mai karfi a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Jigawa, Kano, da Katsina a yankin arewa.













































