Shugaban Karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano ya kaddamar da wani gagarumin shiri na inganta rayuwar jama’a da kuma bunkasa harkokin tattalin arzikin kasa.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in yada labarai na kamar hukumar Muhammad Salisu ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta kara da cewa shirin wanda shugaban karamar hukumar Hon. Lawan Najume Kabo, ya bayar da Naira 30,000 ga mazauna unguwanni 564 da ke fadin kananan hukumomin goma, wanda ya kai Naira miliyan 16.92.
Haka kuma ya hada da rabon sabbin babura guda goma ga shuwagabannin NNPP na unguwanni domin saukaka musu zirga zirga.
Hon. Kabo, yayin da yake jawabi ga mahalarta taron, ya ce shirin na daga cikin kudirin gwamnatinsa na rage wahalhalun da mutane suke fuskanta sakamakon matsin tattalin arziki da ake fuskanta a Nigeria.












































