NDLEA ta cafke Tramadol da Hodar Iblis na Biliyoyin Naira a Filin Jirgi

imgonline com ua twotoone yw8TyVoEeW 750x430

Hukumar yaki da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce, ta cafke wasu tafin kunshin kayayyaki da ke dauke da hodar iblis da kuma kwayoyin tramadol masu karfin Miligiram 225 da aka boye a cikin madubin mota guda 71 da aka tura zuwa birnin Libreville na kasar Gabon.

Hukumar ta ce, ta kama kayan ne a sashen fitar da kayayyaki na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas, tare da kama mutane uku da ake zargin su na da alaka da kayan.

Wata sanarwa da Daraktan yada labarai na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a yau Lahadi, ruwaito cewa, hukumar ta kama wanda ta ke zargi da yunkurin yin safarar kayan mayen, Ihekweme Osinachi Benedict, wanda ke kula da jigilar kayayyaki, inda aka ci gaba da bincike har aka kama wani wanda ake zargi, Uzochukwu Godspower Chukwurahi.

Solacebase ta ruwaito cewa, hukumar ta ce, ko a ranar Juma’a 1 ga watan nan da muke ciki na Agusta hukumar ta NDLEA ta kama wata ‘yar kasuwa Misis Nwafor Roseann Nneka wadda ke da shago a rukunin kasuwanni da ke Ojo, a Legas, biyo bayan kama hodar ibilis gram 100 da kuma wani karin gram 300 na phenacetine, wanda aka boye a cikin Jan-baki na mata wanda ake shirin yin safararsa zuwa Malabo, da ke kasar Equatorial Guinea, inda aka cafe matar a filin jirgi Legas.

Sanarwar ta kara da cewa, a baya an kama wasu jami’an jigilar kaya guda biyu da ke da alaka da jigilar kaya kafin a kama Nneka, wadda ke gudanar da safarar miyagun kwayoyi tare da mijinta, Remigus Nwafor.

A cikin bayanin ta, Misis Nwafor ta yarda cewa ta sayi fakitan Jan-bakin wadanda ake amfani da su don boye haramtattun kwayoyi yayin da mijinta ke kula da yadda ake boye miyagun kwayoyin.

A Abuja, jami’an hukumar NDLEA da ke gudanar da bincike a karkashin tawagar leken asiri a yankunan Gwarimpa da Jahi da Galadimawa a ranar Laraba, 30 ga watan Yuli, sun kama wasu mutane guda uku da suka kunshi: Sabo Sule mai shekaru 24 da Samuel Nnamdi mai shekaru 28 da Idris Jibrin mai shekaru 28 bisa zarginsu da laifin rarraba haramtattun miyagun kwayoyi a cikin birnin.

An gano jimillar giram 149.8 na wani nau’in tabar wiwi mai ƙarfi a wajensu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here