Asusun Tallafin Gidaje: Majalisar Wakilai Sun Yi Barazanar Cafko Atoni-Janar.

Reps

Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken rashin aikewa da asusun ajiyar gidaje na kasa (NHF) da kuma yadda ake amfani da kudaden, ya ce dole ne Akanta Janar ta Tarayya uwargida Oluwatoyin Madein ta bayyana a gabanta.

Kwamitin ya ce ta bayyana a gaban sa ranar 7 ga watan Satumba ko kuma ta fuskanci sammacin kama ta.

Kwamitin ya bayyana haka ne lokacin da Daraktan Hukumar IPPIS ya bayyana a gabansa kan rashin turawa asusun tallafin gidajen NHF.

Kwamitin ya gayyaci IPPIS, wani sashe a ofishin atoni janar don bayyana dalilin da ya sa ba ta aika da asusun ba.

Sai dai kuma, saboda bayanin da daraktan IPPIS ya bayar, kwamitin ya ce AGF ta bayyana a gabanta.

Kwamitin ya ce daraktan IPPIS ba zai iya amsa yawancin tambayoyin da aka yi masa ba, ya ce ya kamata ya zo da AGF kuma dole ne ya shirya yin karin bayani a ranar 7 ga Satumba.

Shugaban kwamitin Rep. Dachung Bagos ya ce, “Ba za muyi la’akari da mutumin da ya kasa ba mu bayanan da muke bukata daga ofishin Akanta Janar na Tarayya ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa IPPIS ta yi ikirarin cewa yana samun kalubale wajen turawa NHF.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here