Hukumar ACRESAL ta bukaci mazauna Kano da su daina sare bishiyu domin kare muhalli.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa, Jami’in kula da ayyukan ACReSAL a jihar Kano, Dokta Dahir M. Hashim ne ya yi wannan kiran ya yin wani taro da masu ruwa da tsaki da ya yi ranar Alhamis a garin Fajewa da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Dr. Dahir wanda Alhaji Muktar Bello ya wakilta ya ce itatuwa na taka muhimmiyar rawa a harkokin tattalin arziki da zaman takewa da kuma daidaita yanayin iska.
“Rashin bashiyu ko sare su na kawo tsananin zafi, ko in ce dimamar yanayi wanda ka iya addabar al’umma da kuma dabbobi.”
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su ba da goyon bayan su wajen aikin gina madatsar ruwa da sauran ayyukan raya kasa da hukumar ACReSAL Zata samar a yankin na Fajewa.
“Ina rokon ku da ku bamu hadin kai wajan wadannan ayyukan da zamuyi a wanann gari, domin hadin kan ku nada mutukar amfani a gare mu.”
A cewarsa, Agro Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACRESAL) wani shiri ne na bankin duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kano, domin taimakawa garuruwan dake fama da kamfan ruwa, zaizayar kasa da sauran matsalolin da suke addabi al’umman jihohin Arewa.
A nasa bangaren Hakimin Takai, Alhaji Yusif Abbas ya ce kofofinsa a bude suke domin bada tallafi idan bukatar hakan ta taso.
“A shirye nake na ba ku duk wani tallafi; ƙofofina a buɗe suke gare ku, zaku iya tuntubata a kowa ne lokaci. ”
Rakiya Umar mazauniyar garin Fajewa ta godewa Allah da gwamnatin Kano da ta kawo musu wannan babban aikin garin su.
“Na yi matukar farin ciki da wannan aikin, kuma ina rokon Allah yasa a fara lafiya a kuma gama shi lafiya.”