Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta dakatar da Gabon daga cikinta bayan juyin-mulkin sojoji na ranar Laraba, wanda ta yi alla-wadai.
Wannan mataki ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin tsaro da zaman lafiya na ƙungiyar ya gudanar a jiya Alhamis.
Kafin dakatarwar sojojin da suka ƙwace mulki a Gabon sun ce za su kafa gwamnatin riƙo bayan hamɓarar da Shugaba Ali Bongo.
Sai dai sojojin ba su shaida tsawon lokacin da za su zauna a mulki ba kafin mayar da ƙasar hannun farar-hula.
Babbar jam’iyyar adawar ƙasar ta buƙaci a yi zaman sulhu domin sannin inda ƙasar ta dosa.
Jam’iyyar na cewa al’ummar Gabon sun yi murnar ganin an kawar da zuri’ar Bongo da suka shafe sama da shekaru 50 suna mulkar ƙasar. Sai dai kuma sun buƙaci sojoji su yi abin da ya dace domin ci gaban ƙasar.