Yadda zaku yi bikin zagayowar haihuwata – Kashim Shettima

Vice President Kashim Shettima 700x430
Vice President Kashim Shettima 700x430

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bukaci abokansa da ‘yan siyasa da su guji sanya sakon murnar zagayowar ranar haihuwar sa a Jaridu.

Shettima ya ba da wannan shawarar ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kan sa ta hannun Mista Olusola Abiola, Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, ranar Alhamis a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shettima zai cika shekaru 57 a ranar Asabar.

Ya kuma shawarci abokansa da su daina amfani da tashoshi da ake biya domin isar da gaisuwarsu a kokarinsu na tunawa da ranar haihuwarsa.

Shettima ya bayyana cewa an yanke wannan shawarar ne bisa la’akari da sadaukarwar da kasa ke yi na kula da albarkatun kasa da kuma tafiyar da harkokin mulki.

Shettima ya kuma bukaci abokansa da su ba shi hadin kai wajen gudanar da ayyukansu na hadin gwiwa zuwa ga wata manufa ta gari.

Ya ce: “Maimakon ku kashe kudi wajen irin wadannan sakonni, ina kara muku kwarin gwiwa da ku ba da gudummawa ga ci gaban al’ummarmu ta hanyar ba da gudummawa ga kungiyoyin agaji, masu bukata ta musamman da sauran mabukata.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here