Zargin cin hancin miliyan 5.2: NSCDC ta bada umarnin a tsare wasu jami’anta 

images 10 4 678x430

Babban kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC) Dr Ahmed Audi ya bayar da umarnin tsare jami’an da ake zargi da karbar naira miliyan 5.2 daga hannun wasu matafiya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NSCDC, Afolabi Babawale, ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa tsarewar ya biyo bayan umarnin binciken da ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayar.

Wani labari da aka yada a shafukan sada zumunta ya yi zargin cewa wasu jami’an NSCDC sun karbi Naira miliyan 5.2 daga hannun wasu samari da suka taso daga Ado-Ekiti, Ekiti zuwa Akure, jihar Ondo.

Karin karatu: Sojoji sun kama wani mutum bisa zargin yin garkuwa da mutane a Kano, tare da kwato makamai

Audi ya bayar da umarnin a kai wadanda ake zargin zuwa hedikwatar NSCDC ta kasa da ke Abuja domin ci gaba da bincike.

Ya ce hakan zai baiwa kwamitin ladabtarwa na hukumar damar gudanar da cikakken bincike kan rahoton karbar kudaden da ake zargin sun yi kamar yadda ministan ya umarta.

“Ayyukan da suka yi ya kasance abin Allah wadai da rashin da’a saboda ya saba wa ka’idar da’a da tsarin aiki (SOP) na NSCDC.

Audi ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ladabtar da duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here