Dele Farotimi, lauya mai kare hakkin dan Adam da ake zargi da bata suna ga babban lauya, Afe Babalola, an sako shi daga gidan yari a Ekiti.
Omoyele Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), ne ya bayyana wannan labari a shafinsa na X ranar Talata.
A cikin sakonsa, Sowore ya rubuta cewa: “Ina farin cikin sanar da cewa Dele Farotimi ba ya hannun gidan yari a Ekiti kuma yana kan hanyarsa ta komawa Lagos.”
Ya kara da cewa, “Gwaggwarmaya tana ci gaba! Barkan ku da hutun karshen shekara.”