Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da wasu mutane tara da ake zargi da hannu a wani mummunan harin da aka kai a garin Yelwata da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue da kuma wasu sassan jihar Filato.
Mutanen tara wadanda aka bayyana sunayensu a matsayin wadanda ake tuhuma a tuhume-tuhume guda shida, an gabatar da su a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Laraba.
Sauran zarge-zargen da aka gabatar a kansu sun hada da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma yin mu’amala da bindigogi, da taimakawa a ayyukan ta’addanci da dai sauransu.
Lauyan DSS, Calistus Eze, ya sanar da kotun cewa an rubuta tuhume-tuhumen da aka gabatar a ranar 28 ga watan Agusta.
A tuhume-tuhume uku masu lamba: FHC/ABJ/CR/449/2025 da aka shigar da Haruna Adamu da Muhammad Abdullahi na karamar hukumar Awe ta Nasarawa da sauran su, ana zarginsu da kai hare-hare a ranar 13 ga watan Yuni a kan mutanen kauyukan Abinsi da Yelwata.
Hukumar DSS ta kama masu garkuwa da mutane da suka kashe wanda suka sace a Kano
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa harin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da jikkata wasu da dama, sannan daruruwa suka rasa matsugunansu a jihohin biyu.
Laifin, inji DSS, ya sabawa sashe na 12 na dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022.
Mutanen biyu da ake zargin sun hada baki ne da Musa Beniyon, Bako Malowa, Ibrahim Tunga, Asara Ahnadu, Legu Musa, Adamu Yale, Boddi Ayuba, Pyeure Damina da sauran su domin kai harin a Yelwata.
Bayan wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, Mai shari’a Nwite ta bayar da umarnin a tsare su a hannun DSS tare da ba su dama ga lauyoyinsu.
Dangane da tuhumar da ake yi wa Ashuwa, Alede, da Halima Umar, Mai shari’a Nwite ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 2 ga watan Oktoba.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da shari’ar Manjo da Tali har zuwa ranar 17 ga watan Oktoba domin nazari.
Ya kuma dage shari’ar Antu da Oloche zuwa ranar 17 ga watan Oktoba.
A halin da ake ciki, hukumar DSS ta shigar da sabbin tuhume-tuhume biyar a kan wadanda ake zargi da kama su da bindigogin M16 guda bakwai da suka haɗa da Huzaifa Ahmad Haruna (Huzaifa Dogo) (NAN).













































