Gobara ta kone ginin makarantar kwalejin kimiyya da fasaha a Kano

Gobara, kone, ginin, makarantar, kwalejin kimiyya
Wani gini na makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano ya kone kurmus sakamakon wata gobara da ta tashi a ranar Talata. Rahotanni sun bayyana cewa...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Wani gini na makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano ya kone kurmus sakamakon wata gobara da ta tashi a ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta lakume daukacin sashen fasaha da masana’antu na kwalejin kimiyya da fasaha.

Karin labari: Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba a matsayin hutun tunawa da Dimokuradiyyar bana

Yayin da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abudullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

Ya kara da cewa ba za a iya tantance bayanan asarar da aka samu nan take ba saboda ana ci gaba da bincike.

Duk da haka, ya yi alkawarin bayyana abinda ya faru bayan kammala binciken.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here